LABARAN DUNIYA
Hukumomin a jahar borno sun fara mayar da yan gudun hijira gidajensu ✍️Daga Umar Adam Bichi Gwamnatin jahar borno ta fara mayar da yan gudun hijira gidajensu biyo bayan rabasu ta ta'addacin boko haram yayi da gidajensu, wannan yunkurin dai ya fara ne da mutanen garin baga inda ahalin yanzu mutane 30 ne suka samu damar komawa gidajen nasu Munsamu zarafin tattaunawa ne da daya daga cikin yan gudun hijirar mesunan Abubakar Umar ya bayyana mana yadda suke cigaba da samun barazanar Boko Haram din a inda aka kyallacesu Yace Boko Haram din na bayyana musu cewa muddun basu raba da inda jami'an tsaro sukeba Fatanmu mudai Allah yakawo karshen ta addanci a Nigeriya dama duniya baki daya